Siyasa
Borno: Ƴan daba sun farmaki tawagar yaƙin neman zaɓen Atiku

Wasu matasa da ake kyautata zaton ƴan daba ne, sun farmaki jerin gwanon motocin ɗan takaran shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen baɗi Alhaji Atiku Abubakar a jihar Borno.
Rahotonni sun bayyana cewa, matasan sun kai harin ne dai-dai lokacin da motocin ke kan hanyar su ta zuwa dandalin taro na Ramat Square da ke Maiduguri babban birnin jihar ta Borno domin Atikun yi wa magoya bayansa jawabi.
Yayin farmakin dai mutanen sun farfasa wasu motocin da ke cikin jerin gwanon tare da raunata mutane da dama.
BBC ta ruwaito cewa, a wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga motoci da dama na yaƙin neman zaɓen Atiku waɗanda aka fasa musu gilasai.