Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da hukuncin da ya samu shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa da laifin raina kotu.
Alƙalin kotun mai shari’a Chizoba Oji, ce ta ya yi watsi da hukuncin yau Alhamis, bayan da ta saurari ƙorafin da shugaban hukumar ta yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ya shigar.
Haka kuma Kotun ta ce, ta gano cewa ba za a iya cewa shugaban na EFCC ya raina kotu ba kasancewar ya riga ya bayar da umurnin a mayar wa wanda ya shigar da ƙarar motarsa ƙirar Range Rover.
Kotun ta ce takardu sun nuna cewa an fara shirin mayar wa mai ƙorafin motarsa da kuma kuɗi naira miliyan 40.
Idan za a iya tunawa dai, a ranar Talata da ta gabata ne mai shari’a Chizoba Oji ta yanke hukuncin cewar EFCC ta raina kotu ta hanyar ƙin bin umurnin hukuncin da ya ce a mayar wa wani mutum motarsa da kuma kuɗi naira miliyan arba’in.
