Kannywood
Halima Atete za ta yi aure Asabar mai zuwa

Fitacciyar Jarumar masan’antar shirya fina-finai ta Kannywood Halima Yusuf da aka fi sani da Halima Atete, na shirye-shirye yin aure kamar yadda jaridar Alfijir ta ruwaito.
A yau Lahadi ne Katin gayyatar ɗaurin auren nata da kuma yadda sauran shagulgulan bikin za su kasance har ma da hotunan kafin aure watau Free Wedding Pictures suka fantsama duniya.
Za a daura auren Jarumar da Angonta Mohammed Mohammed Kala, ne a ranar Asabar mai zuwa 26 ga watan Nuwamba da misalin karfe 10:30 na safe a Maiduguri babban birnin Jihar Borno.