Labarai
Hukumar NIS Ta Ceto Mutanen Da Ake Kokarin Safarar Su A Jigawa

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta ceto wasu mutane takwas da ake zargi ana yunkurin safarar su a jihar Jigawa.
Kwanturolan hukumar NIS reshen jihar Jigawa, Ahmad Dauda Bagari ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a ofishinsa a ranar Litinin.
Ya ce jami’an NIS ne suka yi nasar kubutar da mutanen a ranar Lahadi a kan hanyarsu ta tsallakawa Nijar kan iyakar Kaya-Daurawa a karamar hukumar Roni.
Wadanda abin ya shafa sun hada da maza biyar da mata uku daga jihohi hudu na Abia, Edo, Imo, da kuma Ogun.
Ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa, na da shekaru tsakanin shekaru 19 zuwa 45, ba su da ingantattun takardun izinin tafiya.
Nagari ya kuma bayyana cewa babu wani abu da aka samu na laifi ko kwaya a hannunsu.
Ya ce bayan bincike za a mika wadanda abin ya shafa ga hukumar NAPTIP domin ci gaba da daukar mataki.