Labarai
Shugaba Buhari zai ƙaddamar da sababbin kuɗi a gobe Laraba

A gobe Laraba ne Sshugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi na Naira 1,000 da 500 da kuma 200 waɗanda aka sauya wa fasali.
Gwamnan babban bankin ƙasa CBN Godwin Emefele, ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau Talata a taron kwamitin tsare-tsare na harkokin kuɗi.
Ya ce, babban bankin na CBN ba zai sauya ranar ƙarshe da ya sanya tun da fari na mayar da tsoffin kuɗin zuwa ban kuna domin sauya su da sababbi ba.
Mista Emefele, Ya kuma ce, a goben shugaba Buhari zai ƙaddamar da sababbin kuɗin ne a taron majalisar zartaswa.