Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Da Yasa Fannin Kiwon Lafiya Baya Aiki Yadda Ya Kamata

 

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce karancin kudade ga fannin kiwon lafiya a matakin farko, karanci da rashin rarraba ma’aikatan kiwon lafiya, gurbacewar ababen more rayuwa da kuma raunin tsarin sadarwa sun takaita ci gaban fannin PHC a kasar nan.

Ya bayyana hakan ne jiya a Abuja yayin taron tattaunawa kan harkokin kiwon lafiya na kasa da cibiyar kirkire-kirkire da ci gaban aikin jarida da kuma jaridun Premium Times suka shirya mai taken ‘Role of State and Non-state Actors in Primary Health Care Financing’ wato Gudunmawar Jiha da ƴan Jihohin da ma wadanda ba yan Jihar ba a cikin Tallafin Kiwon Lafiya na matakin Farko’

Ya ce rahotannin asusun kiwon lafiya na kasa da aka buga a cikin shekaru goma da suka gabata sun nuna cewa kudaden da ake kashewa a fannin kiwon lafiya a matakin farko sun yi kadan, tare da kashe makudan kudade kan kiwon lafiya.

Ya kara da cewa “Rashin isassun kudade na tsarin kiwon lafiya na farko ya haifar da mummunar tasiri ga samar da ayyuka kamar rigakafi da kula da lafiyar mata da yara,” in ji shi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Ehanire, wanda Dokta Ngozi Azodo ta ma’aikatar ta wakilta, ya ce kwakkwaran bayar da tallafin kula da lafiya a matakin farko a Najeriya na bukatar hadin gwiwa da jihohin da ma wadanda ba na jiha ba.

Ya ce yayin da masu rike da madafun iko a gwamnati ke ci gaba da taka rawar gani don tabbatar da cewa an samar da albarkatun jama’a don tsarin kiwon lafiya a matakin farko, wani gagarumin kaso na ci gaban da aka samu tare da samar da kudade don kula da kiwon lafiya a matakin farko ya dogara ne da gudunmawar wadanda ba na jiha ba.

Ya ce kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyin fararen hula, kungiyoyi masu zaman kansu, kafafen yada labarai, kungiyoyin addini, kungiyoyin kwadago, kungiyoyin kwararru, jami’o’i, kungiyoyin al’umma da ’yan kasa masu zaman kansu za su iya ba da gudummawa wajen bayar da tallafin kiwon lafiya matakin farko a kasar nan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet