Ilimi
Rabin Albashi: Malaman Jami’ar Maiduguri Sun Yi Barazana Hana Sakamakon Jarabawa

Malaman Jami’ar Maiduguri (UniMaid) sun ce ba za su gabatar da sakamakon jarabawa ko fitar da sakamakon karshe na daliban ba har sai gwamnatin tarayya ta warware matsalar biyan albashi da kuma rashin biyansu albashin watanni 8.
Shugaban kungiyar malaman jami’o’in ASUU reshen jami’ar Unimaid Dakta Abubakar Mshelia Saidu ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Maiduguri ranar Talata.
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa jami’ar ta fara jarabawar dalibai na shekarar 2020/2022 sakamakon dakatar da yajin aikin da ASUU ta yi.
Saidu ya ce, “Mambobin ASUU ba za su yi rajistar rubuta jarabawar da ake yi a yanzu ba; Hakanan ba za su gabatar da sakamako zangon karatu na biyun farko da na biyu na zaman karatu na 2020/2021 ba.
“Ba za a yi gasa ba da malamai matsayin ilimi ta masu gudanarwa a sashe na 1-4, 5 ko 6, kamar yadda ya dace.
“Gwamnati ta ce ‘ba aiki, ba biya; mu ce ‘ba biya, ba-aiki.”