Kasuwanci
Shugaban Kasa Buhari Ya Kaddamar Da Sabbin Kudin Najeriya

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da sabbin kudin Najeriya da aka sake musu fasali, wato dai aka yi musu kwaskwarima.
Jaridar KAKAKIHAUSA ta rawaito cewa kudin da aka sauyawa fasali sun haɗar da, 200, 500, 1000.
Ƙaddamar da sabbin takardun kudin ya gudana ne yau a Abuja, babban birnin tarayya, wanda ya gudana gaban yan majalisar wakilan kasar.
Yanzu haka dai nan da zuwa watan Disamba ake sa ran fara amfani da kudin, kamar dai yadda gwamnan bankin kasar Godwin Emefele ya tabbatarwa da yan kasar.