Ilimi
Dole Ne A Sake Duba Fannin Ilimi A Makarantun Gwamnati – Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce dole ne gwamnatoci a kowane mataki su kara saka hannun jari a makarantun gwamnati domin inganta harkar ilimi a kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a babban taron kacici-kacici na kasa na shekarar 2022 da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokaradiyya ta kasa (NILDS) ta shirya a Abuja ranar Alhamis.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa gasar ta gudana ne a kan “Majalisar dokoki da Dimokuradiyya” da aka shirya wa makarantun sakandare a fadin babban birnin tarayya Abuja da shiyyoyi shida na siyasar kasar nan.
A nasa jawabin, Lawan ya ce dole ne a kara zuba jari domin inganta makarantun gwamnati a fadin kasar nan.
“Ina jin cewa makarantun gwamnati ba su da kyau idan aka kwatanta da makarantu masu zaman kansu.
“A cikin makarantu bakwai na wannan gasar kacici-kacici, uku ne kawai makarantun gwamnati da makarantu masu zaman kansu hudu. Kuma wannan abun bada labari ne.
“Labarin ya nuna min cewa makarantunmu masu zaman kansu sun fi samun nasara don haka za su iya cin nasara tare da doke makarantun gwamnati.
“Wannan yana da matukar muhimmanci a gare mu. Kira ne na mu tashi mu farka. Dole ne gwamnati ta saka hannun jari a makarantunmu na gwamnati,” inji shi.