Connect with us

Labarai

Kotun ƙoli ta yi watsi da buƙatar A. A Zaura

Kotun kolin ƙasar nan, taki amincewa da buƙatun ƙan takarar Sanatan Kano ta tsakiya na jam’iyyar APC, Abdulsalam Sale Abdulkarim wanda aka fi sani da A. A Zaura, na dakatar da babbar kotun tarayya daga yi masa shari’a.

Kotun ta ba da umarnin ta hannun lauyan hukumar ta EFCC, I.G Waru a ranar Alhamis, 24 ga Nuwambar Shekarar 2022.

Kotun kolin ta kuma umarci dan takarar Sanatan da ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya ta Kano, domin fuskantar tuhume-tuhumen da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ke yi masa.

Hukumar dai tana tuhumar A.A Zaura ne bisa zargin damfarar wani dan kasar Kuwaiti ta hanyar karbar kudi dalar Amurka miliyan 1 da Dubu 320, bisa zargin cewa yana sana’ar gine-gine a Dubai da Kuwait da sauran kasashen Larabawa.

Tun a ranar 9 ga watan Yunin Shekarar 2020, Mai Shari’a Justice Allagoa ya samu wanda ake kara ba shi da laifi kuma ya sallame shi kan dukkan tuhume-tuhumen.

A bisa rashin gamsuwa da hukuncin da karamar kotun ta yanke, Lauyan da ke kare masu kara Musa Isah ya daukaka kara a wani yunkuri na soke hukuncin da kotun baya ta yanke.

Sakamakon haka, a wani mataki na bai-ɗaya da alƙalan kotun uku suka yanke inda mai shari’a Abdullahi M. Bayero ya yanke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet