Connect with us

Labarai

An rantsar da Sanata Ademola Adeleke a matsayin sabon gwamnan jihar Osun

Sabon Gwamnan jihar Osun Sanata Ademola Adeleke da mataimakinsa, Kola Adewusi sun karbi rantsuwar kama aiki.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Babban jojin jihar, mai Sharia Adepele Ojo ya rantsar da mutanen biyu a wani gangamin taron da ya gudana ayau.

Rahotonni sun ce, Sanata Ademola Adeleke, ya shiga wurin taron ne bisa ayarin motoci da misalin ƙarfe 11:20 na safe kuma ya kammala karɓar rantsuwa da karfe 11:50 na safiya.

Wadanda suka halarci taron rantsuwar a filin wasa na birnin Osogbo sun hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da gwamnan jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom.

Sauran su ne Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa, da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi.

Haka kuma a wurin taron an samu halartar uwargidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Titi Atiku, Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, da tsohon gwamnan Oyo, Cif Rashidi Ladoja, da dai sauransu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet