Connect with us

Labarai

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Bashir Shariff A Matsayin Dan Takarar APC

 

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na yankin Yobe ta Arewa.

Kotun ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke zamanta a Damaturun jihar Yobe, ta yanke na cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ba shi ne dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Yobe ta Arewa a zaben shekara mai zuwa a majalisar wakilai ta kasa ba.

Kotun ta gabatar da cewa Mista Lawan bai shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka amince da shi ba domin zaben dan takararta a zaben da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayun 2022.

Da yake yanke hukunci kan karar da shugaban majalisar dattawan ya shigar, kwamitin alkalai mai mutane uku na kotun daukaka kara karkashin jagorancin mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ya ce zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a ranar 9 ga watan Yuni ya ci ya sabawa doka kundin tsarin mulki.

An dai daidaita dokar ne dangane da shigar da Hukumar zabe mai Zlzaman kanta ta Kasa (INEC) a zaben fidda gwani na jam’iyyu, wanda za a sa ido, ba hukumar zabe ta sa ido a zaben fidda gwani na ranar 9 ga watan Yuni ba.

Jam’iyyar APC ta kai kara a kotun daukaka kara da kanta kuma ta fifita dan takara Ahmed Lawan amma ta kasa sanya shi a matsayin mai shigar da kara.

Mista Lawan ya bayyana a cikin karar ne a matsayin mai kara na 2 wanda ya nuna cewa shi da jam’iyyar APC suna aiki tukuru a yayin da suke kokarin cimma wata manufa.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa Wanda ya shigar da kara (APC) zai biya kudi naira miliyan daya ga wanda ake kara na daya (Bashir Sheriff) a matsayin kudin bata lokaci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet