Labarai
Dalilin Da Yasa Yan Daba Suke Kaiwa Ofisoshin INEC Hari — Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya ce dalilin da ya sa masu aikata laifuka ke kai hari tare da kona ofisoshi hukumar zabe ta kasa (INEC) shi ne kawo zagon kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Jaridar Vanguard ta tattaro a jiya cewa wasu ‘yan daba sun kona ofishin INEC da ke karamar hukumar Izzi a jihar Ebonyi ranar Lahadi.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Shehu Sani a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin ya ce maharan makiyan ci gaba ne da ba sa son a gudanar da babban zabe a shekarar 2023.
Ya ce, “Babban makasudin masu kai hari da kona ofisoshin INEC shi ne yin zagon kasa a babban zabe mai zuwa.
“Su makiyan dimokradiyya ne. Hakki ne na kishin kasa mutane su bijire wa tashin hankali kuma su tashi tsaya a kan wadancan ‘yan mulkin kama karya.”