Labarai
Wata Kotu Ta Bada Umarnin A Kai Babban Hafsan Sojin Kasa Gidan Yari

Wata babbar kotu da ke zamanta a Minna a jihar Niger, ta bayar da sammacin kamo babban hafsan sojin kasa, Janar Faruk Yahaya bisa zarginsa da laifin sabawa Umarnin kotu, bisa umarnin Mai shari’a Halima Abdulmalik.
Haka kuma lamarin ya shafi Kwamandan Horar da Rukunin soji dake Minna, Manjo Janar Stevenson Olugbenga Olabanji.
Babbar alkaliyar jihar, Halima Abdulmalik, ta bayyana cewa, umarnin ya biyo bayan sauraron karar da aka shigar gaban kotun, bisa ga doka ta 42, doka ta 10 na dokar kare farar hula ta babbar kotun jihar Neja ta shekarar 2018.
Mai shari’a Halima Abdulmalik ta bayyana cewa: “Kotu na bukatar shugaban hafsan sojin kasa, Janar Faruk Yahaya da kwamandan horas da sojojin na Minna, Manjo Janar Stevenson Olugbenga Olabanji, a tsare a gidan yari na Minna domin sabawa umarnin wata kotu a ranar 12 ga wata. Oktoba 2022.
Ta ba da umarnin a ci gaba da tsare mutanen biyu a gidan yari har sai sun wanke kansu daga zargin sabawa umarnin kotu.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa Sai dai daga Bisani, Alkaliyar da ke jagorantar shari’ar ta dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Disambar 2022 don ci gaba da sauraron karar.