Connect with us

Labarai

Rikicin Siyasa A Borno: Zulum Ya Bada Umarnin Kama Masu Laifin

 

A fusace kan rikicin siyasa a jihar Borno a ‘yan kwanakin nan musamman ma harin da aka kai wa tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Maiduguri a watan da ya gabata, gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum ya umurci rundunar ‘yan sanda da DSS da su kamo masu laifin ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ta siyasa ba.

Zulum, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Malam Isa Gusau ya fitar a ranar Alhamis, ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno da ya gudanar da bincike tare da tabbatar da kama duk masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya kamar yadda doka ta tanada.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa Ya ce zaman lafiyar al’umma shi ne ginshikin gwamnati don haka ya kamata a samar da tsaro domin jama’a su ci moriyar dimokradiyya.

“Na samu rahotanni kan sabbin rikice-rikice na siyasa a jihar. Ina yin Allah wadai da wadannan munanan al’amura da ba su dace ba, ina kuma umurtar Kwamishinan ‘yan sanda da na DSS da su gaggauta gudanar da bincike tare da tabbatar da duk wanda ke da hannu wajen fuskantar fushin doka.”

“Ina umurtar shugabannin hukumomin tsaro a karkashin hukumar tsaro ta jihar Borno da su gaggauta kiran taro da wakilan manyan jam’iyyun siyasa, musamman APC da PDP, su sanya hannu a kan wasu ayyuka tare da yi musu gargadi kan duk wani tashin hankali tare da daukar matakan ladabtarwa.

“A tabbatar an yi wa duk wani mai laifi, musamman ’yan siyasa da za su iya tayar da hankali, komai girman su hukunci

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet