Connect with us

Labarai

Zamfara: Kotu Ta Bada belin Tsohon Ministan Yada Labarai

 

Kotun Shari’ar Musulunci da ke jihar Zamfara ta bayar da belin tsohon Ministan yada labarai, Ikra Bilbis.

‘Yan sanda sun kama Bilbis a ranar Talatar da ta gabata, inda aka gurfanar da shia gaban kotu bisa zargin lalata allunan tallan jam’iyyar APC da wasu kadarorin gwamnati a yayin wani gangamin jam’iyyar PDP a ranar Lahadi.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai shari’a Jibril Ibrahim, ya ce ya bayar da belin wanda ake tuhumar ne bisa sashe na 300 da na 301 na kundin hukunta laifukan shari’a na jihar Zamfara.

Sai dai ya baiwa wanda ake tuhuma sharudda uku da sai ya cika.

Ya ce, “Bisa la’akari da cewa, mai gabatar da kara da kuma lauyan wanda ake tuhuma James Shaka sun cimma yarjejeniya kuma bisa sashe na 300 da 301 na kundin hukunta laifukan shari’a na bayar da belin wanda ake tuhuma.”

“Duk da haka sai ya cika sharudda masu zuwa:

“Zai kawo masu tsaya masa mutane guda biyu. Daya daga ciki sai an tabbatar babban sakatare a ma’aikatan gwamnatin jihar.

“Dayan wanda zai tsaya masa dole ya samu gida a garin Gusau wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 20 zuwa sama.

Ikra Aliyu Bilbis ya kasance ministan yada labarai a lokacin gwamnatin Goodluck, kuma a halin yanzu yana neman kujerar Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya.

An kama shi ne a ranar Talatar da ta gabata kuma an tsare shi a shedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Gusau bisa zarginsa da hannu wajen lalata allunan tallace-tallacen jam’iyyar APC da wasu kadarorin gwamnati a wani gangami da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Dakta Dauda Lawan Dare ya shirya.

Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, An dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Disambar 2022 don ci gaba da sauraren karar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet