Connect with us

Addini

Hajjin 2022: Ganduje Ya Bukaci Da A Binciki NAHCON Kan Gudanar Da Aikin Hajji

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana aikin Hajjin shekarar 2022 da ya gabata a matsayin mafi muni da ya taba gani a lokacin da yake gwamnan jihar Kano.

Ganduje ya ce ba a gudanar da shi ba yadda ya kamata ba, an lura da wasu halaye na rashin gaskiya, zamba da kuma abubuwan da ba su dace ba a yayin aikin.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abba Anwar, babban sakataren yada labaran gwamnan ya fitar a ranar Juma’ar nan.

A cewar sanarwar, Ganduje ya koka kan halin da ake ciki a gidan gwamnatin Kano, lokacin da ya karbi rahoton aikin Hajji na 2022, a ranar Juma’a. daga hukumar jin dadin alhazai ta Kano, karkashin jagorancin shugaban hukumar Abdullahi Saleh Pakistan da babban sakataren hukumar Abba Muhammad Danbatta.

“Bayan ya taya hukumar alhazai ta jihar murna, bisa namijin kokarin da suke yi wajen gudanar da aikin Hajjin, ya bayyana cewa, “Saboda rashin iya aiki da kuma rashin gudanar da aikin Hajji na kasa, maniyyata da dama sun sha wahala sosai ba tare da wani nadama daga hukumar ta kasa ba”, Sanarwar ta ce.

Ya kuma kara da cewa, saboda rashin gaskiya na hukumar ta kasa, “… ko a matakin hidima, hukumar alhazai ta kasa ta gaza sosai.”

‘’Jirgin da muka zaba ba shi suka ba mu ba. Ni da kaina na je can domin gabatar da korafinmu kuma sun yi alkawarin bin zabin da muka yi. Amma abin takaici sun ba mu wani kamfanin jirgin saman daban daban.”

”An damu da cewa an bar Mahajjata da yawa a kasa ba tare da sun yi aikin Hajjin ba”.

“Kamfanin jirgin da suka ba mu shi ne wanda muka sami matsala, a shekarar da ta gabata, kuma kamfanin ya sayar da guraban da muka ba su. To wannan kamfanin jirgin daya ne, sun ba mu ne saboda rashin aiki da rashin iya gudanar da aikin.

Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, Ko da yake mun gaya musu dalilinmu na kin amincewa da kamfanin jirgin da suka bamu. Sun yi mana alkawarin ba mu zabi, amma sun kasa yin hakan,” ya koka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet