Labarai
Shehu Sani Ya Alakanta Wawure Kudaden Kananan Hukumomi Da Cewa Da Sanin EFCC Da ICPC

Tsohon dan majalisar wakilan kasar nan, Sanata Shehu Sani, ya yi Allah wadai da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta Kasa ICPC, kan karkatar da kudaden kananan hukumomi ga gwamnatocin jihohi.
Sanata Shehu Sani ya bayyana damuwarsa ne a ranar Lahadi a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter.
KakakiHausa cewa a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta zargi gwamnonin jihohi da karkatar da kudaden kananan hukumomi.
Shugaban kasar ya yi wani taron a ranar Alhamis ya yi zargin cewa wasu gwamnonin jihohi suna karkatar da kason kudi zuwa kananan hukumomin da aka aika daga asusun tarayya.
Jaridar DailyPost ta rawaoto cewa, Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya yi fatali da wannan ikirari da Gwamnatin Tarayya ta yi, inda ya ce kamata ya yi ta fito fili ta hanyar bayyana sunayen wadanda suka aikata laifin, maimakon yin tuhume-tuhume.
A halin da ake ciki kuma, Sani, wani fitaccen mai sukar lamirin al’umma ya yi wani ra’ayi na daban, yana mai cewa ba zai yiwu a karkatar da kudaden kananan hukumomi ba tare da sanin EFCC da ICPC ba.
Ya rubuta: “Ba zai yiwu a karkatar da kudaden kananan hukumomi zuwa ga gwamnatocin jihohi ba tare da sanin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ba.
“Babu wani makudan kudade da za su iya tafiya a cikin tsarin banki ba tare da gaggafa ko idanu ba. Idan suna son dakatarwa za su iya.