Connect with us

Labarai

Matsalar tsaro ta sanya Hukumar INEC sauya cibiyoyin zaɓe 16 a jihar Yobe

Hukumar zaɓe mai kaman kanta ta Najeriya INEC, ta bayyana shirinta na sauya wa wasu cibiyoyin zaɓe guda goma sha shida a ƙananan hukumomi uku da ke fuskantar kalubalen tsaro a jihar Yobe wurare.

Shugaban ayyuka na hukumar Alhaji Goni Usman, ne ya bayyana hakan da yammacin Talatar makon nan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Ya ce, za a kwashe cibiyoyin ne daga ƙananan hukumomin Geidam da Yunusari da Gujba zuwa wuraren da suke da cikakken tsaro.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa jami’in ya ce, an mayar da kuri’u 1,109 zuwa rumfunan zaɓe, wanda hakan ya mayar adadin rumfunan zaɓen jihar zuwa 2,814.

A jawabinsa, Shugaban sashen fasaha na hukumar Alhaji Lamido Ibrahim, ya ce, adadin tsofaffi da sabbin katinan zaɓe guda 93,912 ne hukumar ta tattara daga shekarar 2019 zuwa bana.

Haka kuma ya ƙara da cewa, zuwa yanzu an raba guda dubu 49,399, yayin da adadin 44,513 suke a hannun hukumar kasancewar masu su ba su karɓa ba.

Alhaji Lamido Ibrahim, ya kuma yi kira ga waɗanda suka cancanci kaɗa kuri’a da ba su karɓi katin zaɓen nasu ba da su hanzarta domin yin amfani da su a zaɓen baɗi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet