Labarai
Hukumar NDDC Ta Raba Kayan Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

Hukumar raya yankin Neja Delta ta fara rabon kayan agaji ga al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Imo.
Da yake jawabi yayin mika ragamar gudanarwa a ofishin NDDC na jihar Imo, dake Owerri, a ranar Larabar, mukaddashin Manajan Daraktan hukumar, Emmanuel Audu-Ohwavborua, ya ce hakan na daga cikin matakan da hukumar ta NDDC ta dauka na rage radadin al’ummar yankunan da abin ya shafa.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hukumar NDDC, Dokta Ibitoye Abosede, ya fitar kuma ya rabawa wa manema labarai a Fatakwal ranar Laraba.
Audu-Ohwavborua, wanda ya samu wakilcin Daraktan Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Jama’a, Dokta George Uzonwanne, ya ce matakin na ci gaba da shiga tsakani domin tallafawa al’umma.
A wani bangare sanarwar ta kara da cewa, “Muna fatan wadannan kayayyakin agaji za su taimaka wajen dakile illolin ambaliya da kuma bayar da tallafi ga wadanda ambaliyar ta shafa, musamman a wannan lokacin na bukukuwan karshen shekara.
“Muna kuma shirye-shiryen kaddamar da shirin kiwon lafiya kyauta na yankin mu. ”
“Aikin jinya kyauta a halin yanzu, muna kan hanyar sayo kayayyaki kuma za mu tabbatar da cewa mun yi aiki kafada da kafada da gwamnatocin jihohi don aiwatar da hakan.”