Labarai
Hukumar Kidaya Ta Tabbatarwa ‘Yan Najeriya Ba Za Ta Basu Kunya Ba

Hukumar kidaya ta kasa, NPC, ba za ta kunyata ‘yan Najeriya ba kan gudanar da kidayar jama’a da gidaje na kasa na shekarar 2023 da aka shirya gudanarwa a watan Afrilu. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Wannan tabbacin ya fito ne daga bakin kwamishinan hukumar na jihar Kwara, Malam Abdulrazaq Gidado, a wajen fara wani horo na kwanaki biyar ga jami’an CAPI masu taimakawa 65 na wayar da kan jama’a a Ilorin ranar Juma’a.
Da yake bayyana shirin horaswar, Gidado ya ce, an zabo jami’an ne ba bisa nuna sani ba, sai dai saboda karfin da suke da shi na samar da sakamakon da ake bukata ga hukumar.
Ya bayyana cewa, zabo mutanen zai yi tasiri kan ilimin fasahar da akwai a cikin shirin kan kidayar jama’a da za a fara a fadin kasar nan.
Kwamishinan na tarayya ya bukaci jami’an da su dauki horon da suke yi da muhimmanci tare da baiwa hukumar iya kokarinsu domin samun nasarar aikin kidayar jama’a.
Gidado ya ce hukumar ba kawai a shirye take ta kawar da duk wanda aka samu yana son rai ba, amma ba za ta gajiya ba, ko kuma ta bar duk wani abu da zai kawo cikas ga manufar hukumar ta gudanar da aikin kidayar jama’a mai karbuwa, sahihi da kuma gaskiya ga kasar nan.
An zabo mutane hudu daga kowace kananan hukumomi 16 na jihar domin gudanar da shirin horaswa.