Labarai
Hukumar KAROTA Ta Kama Masu Laifi Samada Da 3200 A Shekarar 2022

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA ta kama masu laifi 3,245 daga watan Janairu zuwa Disambar 2022.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Nabilusi Abubakar, ya fitar ranar Juma’a a Kano.
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa an sami ragin masu aikata laifin a shekarar 2022, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata da KAROTA ta samu masu laifi 7,835.
A cewar sanarwar, “a shekarar da ake shirin bankwana da ita, hukumar ta yi nasarar yi wa jimillan masu kekuna adaidata sahu 52,242 rajista a karkashin tsarin ba da izinin tuki na Kano.
“Wannan rajistar tana da matukar muhimmanci a gare mu, don haka duk wanda aka yi wa babur mai kafa ukun da aka rajistar ba zai yi amfani da ita wajen aikata laifi ba, ya sani sarai za a kama shi.
“Ya zuwa yanzu an kama baragurbi da yawa daga cikin masu adaidaita sahun.
“Tare da rajistar mun sami nasarar gano tare da kama masu satar wayar da ke tsorata mutane a jihar, suna amfani da babur mai kafa uku wajen aikata irin wadannan laifuka.
“KAROTA ta samu nasarar daukar sabbin ma’aikata sama da 500 wanda hakan ya kara mana kwarin gwiwa a jihar musamman a cikin babban birnin jihar tare da samar da sabbin ofisoshin shiyya a Tudun Wada da Doguwa,” inji shi.
Abubakar ya ci gaba da bayanin cewa a cikin shekarar majalisar dokokin jihar ta zartar da dokar hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, ta 2022 (gyara mai lamba daya).
Ya kara da cewa da dokar za ta gudanar da ayyukanta cikin kwanciyar hankali a jihar.
“Ta hannun sashin shari’ar mu, hukumar ta samu takardar sammacin kotu na samun nasarar rusa haramtattun gine-ginen da suka toshe hanyoyi a cikin kwaryar birni da kuma wasu manyan kasuwanni wadanda suka hana zirga-zirgar ababen hawa.
“Duk wanda ya kafa duk wani tsari na doka akan kowane titinan mu ba zai tsira ba,” in ji shi.
Ya nuna godiya ga jama’a tare da ba su tabbacin za su zage damtse wajen yin aiki a shekara mai zuwa don kare su yayin amfani da hanyoyin. (NAN)