Connect with us

Labarai

Ni Da Kaina Nayi Murabus Tun Kafin Gwamnatin Kano Ta Kore Ni — Baba Impossible

Tsohon kwamishinan al’amuran addinai na jihar Kano Dr Muhammad Tahar Adam Baba Impossible ya ce ya yi mamakin karyar da gwamnantin Kano ta kitsa kan batun korarsa.

Baba Impossible ya yi wannan jawabinne ta cikin wani sakon murya da ya aikewa manema labarai da yammacin yau.

Ya ce tun ranar Juma’ar da ta gabata ya rubuta takardar barin aiki, ya kuma kaiwa sakataren gwamnatin Kano da Shugaban ma’aikata aka kuma karba aka saka masa hannu.

Sai dai ya ce ga mamakinsa sai gani ya yi a kafafen yada labarai cewa gwamnatin Kano ta kore shi.

”Bayan an kore ni ne aka karbi takardar tawa? Ko Kuma bayan na mika takardar aka koreni? A cewar Baba Impossible.

Ya ce sun dai bar wannan zance a haka amma idan gwamnati ta ci gaba da magana a kai to shi ma zai dora da zancensa.

Idan za a iya tunawa da safiyar ranar Asabar ne gwamnatin Kano ta sanar da korar Kwamishinan daga aiki, cikin wata sanarwa da ta fitar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet