Connect with us

Labarai

Al’ummar Brazil na yin bankwana da gawar marigayi Pele

Yanzu haka al’ummar ƙasar Brazil suna can suna yi wa gawar fitaccen tsohon ɗan wasan duniyar Pele bankwana tare da girmamawar ƙarshe kafin yi masa jana’iza gobe Talata.

An ajiye gawar marigayin ne yau Litinin a tsakiyar filin wasa na Urbano Caldeira, wanda ya kasance filin wasan tsohuwar ƙungiyarsa ta Santos.

BBC ta ruwaito cewa, dubban ɗaruruwan magoya bayan tsohon ɗan wasan sun fara bin dogayen layuka ɗauke da tutoci da hotunan marigayin wanda ya lashe kofin duniya har sau uku, inda suke shiga filin wasan domin yin ban kwanan ƙarshe da gawar.

Haka kuma ta ruwaito cewa, Za a fara shirye-shiryen yi wa gawar tsohon ɗan wasan ranar Talata, inda za a ɗauki gawar Pele a zagaya da ita kan titunan birnin Santos, ciki har da kan titin da gidan mahaifiyarsa Celeste Arantes mai shekara 100 ta ke zaune.

Daga bisani kuma bayan kammala zagayen ƴan uwansa za su yi masa jana’iza tare da binni shi a maƙabartar Memorial Necrópole Ecumênica cemetery, kamar yadda kafar ta bayyana.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet