Labarai
Wasu Mahara Sun Kona Ma’aikacin CBN, Da Matarsa, Sun Sace Dansu

Wasu ‘yan bindiga sun kashe Kehinde Fatinoye, ma’aikacin babban bankin Kasa CBN.
An kashe Fatinoye ne tare da matarsa, wanda har zuwa lokacin da lamarin ya faru, babban sakatare ne na sirri a Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Abeokuta, FUNAAB.
An tattaro cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki gidan ma’auratan da ke Ibara GRA a ranar Lahadin nan a daidai lokacin da suke dawowa daga bikin sabuwar shekara.
Wata majiya ta shaida wa Daily Post cewa maharan sun kashe ma’auratan tare da cinna musu wuta a cikin gidansu.
Har ila yau, an ce maharan sun tafi da dan ma’auratan da ma’aikatan gidan.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce: “Gaskiya ne lamarin ya faru. An fara bincike. An kama wani da laifin faruwar lamarin. An kashe mutumin da matarsa kuma har yanzu ba mu sami yaronsu da aka tafi da shi ba.”
Ya kuma tabbatar da cewa: “Lamarin ya faru ne bayan karfe 12 na dare. Wannan lamari ne karara na kisan gilla kuma ba za mu bar wani wuri ba don bankado wadanda ke da hannu a kisan.”