Connect with us

Labarai

Gwamna Tambuwal ya sha alwashin gurfanar da mutanen da suka jefi motocinsa

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa motocinsa a jihar tare da shan alwashin ɗaukar matakin gurfanar da mutanen da suka kai harin a gaban kotu.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara a kan harkokin yaɗa labarai Muhammad Bello ya fitar da yammacin yau Talata.

Rahotonni sun bayyana cewa, waɗanda ke cikin tawagar gwamnan yayin da aka kai harin sun haɗa da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Sokoto Malam Sa’idu Umar da Janar Aminu Bande da mataimakin gwamnan Sokoto Sagir Bafarawa.

Sai dai sanarwa ta bayyana cewa cikin ƴan tawagar babu wanda ya ji rauni.

Haka kuma sanarwa ta ce, an lalata motoci guda biyu yayin farmakin.

Gwamna Tambuwal, a ganawarsa da manema labarai, ya ce an kama wasu daga cikin waɗanda suka kai harin kuma za a kai su kotu.

Shafin BBC ya ruwaito cewa, Wasu waɗanda ake kyautata zaton zauna gari banza ne suka yi ruwan duwatsu ga ayarin motocin gwamnan a cikin birnin Sokoto a lokacin da yake komawa birnin daga yaƙin neman zaɓen da yaje Ƙananan hukumomin Wamakko da Silame.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet