Tsaro
Kaduna: Sojoji sun kashe ƴan bindiga 4 tare da ƙwato makamai

Dakarun rundunar Operation Forest Sanity da ke yaƙi da ƴan bindiga a jihar Kaduna, yi nasarar fatattakar wasu ƴan ta’adda hudu tare da ƙwato makamai da alburusai yayin wata arangama da suka yi da su.
Daraktan yaɗa labarai na rundunar Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Talatar makonan.
Danmadami ta cikin sanarwar ya ce, a ranakun Lahadi da Litinin ne sojojin suka amsa kiraye-kiraye kan harin da ƴan bindiga suka kai ƙauyen Rafin Sarki da ke yankin ƙaramar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.
“Bayan dakarun soja sun yi artabu da ƴan ta’addan ne suka yi nasarar kashe mutane biyu, inda suka kwato bindiga ƙirar AK 47 guda ɗaya, inji sa.
Ya ƙara da cewa,”A ranar Talata kuwa dakarun sojoji sun kai wani harin kwantan ɓauna a kauyen Rafin Taba a nan ma an kashe ƴan ta’adda biyu”.
Ya kuma ce a nan ma sojojin sun ƙwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu da alburusai guda 51 da wayoyin hannu guda biyar da babura biyu da kuɗi Naira 206,000.