Labarai
Kwamishina ta yi murabus bayan sauke mahaifinta daga Wazirin Bauchi

Bayan sauke mahaifinta daga sarautar Wazirin Bauchi Kwamishinar Gama Kai da harkokin ƙananan masana’antu ta jihar Bauchi Hajiya Sa’adatu Bello Kirfi, ta yi murabus daga mukaminta.
A wasiƙar ajiye aiki da ta rubuta mai ɗauke da kwanan watan yau Laraba 4 ga watan Janairu, Hajiya Sa’adatu Kirfi, ta bayyana godiyar ta ga gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Abdulkadir bisa ba ta damar yin aiki a ƙunshin gwamnatin sa.
Sai dai tsohuwar Kwamishinar ba ta bayyana dalilin ta na yin murabus ba.
Takardar ta ce, “Mai girma gwamna, ina son miƙa takardar murabus ɗina daga matsayin mamba ta majalisar zartaswar jihar Bauchi kuma kwamishina a ma’aikatar Gama Kai da Kananan masana’antu ta jihar Bauchi nan take.
“Ina son gode wa mai girma gwamna bisa damar da ya bani na yin aiki a karkashin gwamnatinsa.” cewar sanarwar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan jihar ta Bauchi ya kori mahaifinta Alhaji Bello Kirfi daga sarautarsa ta Wazirin Bauchi.