Kasuwanci
Kano: Hukumar NMDFRA ta rufe gidajen Mai 14 bisa sayar da fetur da tsada

Hukumar kula da hada-hadar man fetur a cikin ƙasa ta Najeriya, NMDPRA ta rufe gidajen mai guda 14 a jihar Kano bisa samun su suna sayar da fetur a kan farashin da ya zarta ƙa’ida.
Shugaban hukumar shiyyar Kano Aliyu Muhammad-Sama, ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai yau Alhamis.
Ya ce, sun gano gidajen man ne yayin wani sintiri da hukumar ta gudanar a Alhamis ɗin makon nan inda suka same su suna sayar da litar fetur a kan Naira 290 zuwa 300, don haka ya zama wajibi hukumar ta garƙame su.
Aliyu Muhammad-Sama, ya ƙara da cewa hukuncin gidajen man da aka kulle ɗin shi ne biyan tarar Naira 150,000 bisa duk famfo guda.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, shugaban hukumar ya ƙara da cewa za su ci gaba da kasancewa a kulle har zuwa lokacin da suka biya tara da kuma yarda su sayar da fetur a kan farashin da ya dace.