Labarai
Ƙungiyar NANS ta buƙaci shugaba Buhari ya sanya baki kan ƙarin kuɗin makaranta

Ƙungiyar ɗalibai ta Najeriya NANS, ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya yi gaggawar sanya baki game da ƙarin kuɗin makaranta da jami’o’i ke shirin yi tun gabanin hakan ya haifar da matsaloli.
Sakataren ƙungiyar na ƙasa Usman Baba Kankia, ya ne ya buƙaci hakan a ganawarsa da BBC.
Usman Baba ya ce, ”Duk makarantun gwamnatin tarayya sun yi ƙarin kuɗin makaranta har fiye da kashi 250 cikin dari”.
Kafar ta ruwaito cewa Sakataren ƙungiyar ta NANS ya kuma yi zargin cewa makarantun sun samu umarnin ƙara kuɗin makarantar ne daga sama.
Ya ƙara da cewa, bisa haka ne suka rubuta wasiƙa ga shugaba Buhari suna masu buƙatar shi a matsayinsa na uba da ya sanya baki domin mayar da kuɗin makaranta kamar yadda yake a baya.
Usman Baba Kankia, ya kuma ce, ”Matuƙar ba a soke ƙarin kuɗin makarantar da aka yi ba, to kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na ɗaliban Najeriya ba za su koma makaranta ba, sakamakon rashin kuɗin da za su iya biya.