Labarai
Hukumar DSS Ta Musanta Mamayar Ofishin Gwamnan CBN Emefiele

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta musanta yin dirar mikiya da mamaye ofishin gwamnan babban bankin Kasa, Godwin Emefiele.
An samu labari a wasu kafafen yada labarai (ba The PUNCH ba) cewa hukumar DSS ta mamaye shedikwatar CBN domin cafke gwamnan babban bankin.
A wata sanarwa da kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ya fitar ranar Litinin, hukumar ta musanta kama Emeifele.
Afunanya ya ce, “An jawo hankalin hukumar tsaron kan labarin karyae da ake yadawa cewa jami’anta sun mamaye babban bankin Kasa tare da kokarin kama gwamnansa, a yau 16 ga watan Janairun 2023. Wannan labari ne na karya kuma yaudara ce.”