Featured
Yadda Wasu Mabarata Suka Yi Watsi Da Tsohon Kudin Da Aka Basu Sadaka

Wasu mabarata a babbar hanyar Kano da ke jihar Kaduna sun yi watsi da wata tsohuwar takardar kudin naira 1,000 da wani matashi ya ba su.
Kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito a ranar Larabar matashin wanda ya bayyana sunansa Caleb wasu mabarata guda uku ne suka same shi a kan keken guragu a lokacin da ya fito daga mota da safa inda ya yanke shawarar baiwa mabaratan tsohuwar takardar kudi ta Naira 1000 daga aljihunsa.
Amma ga mamakinsa sai maroka suka juya suka yi tafiyarsu suka bar saurayin, suka ki amincewa su karba.
Sai mutumin ya ce: “Su (mabarata) sun zo mini suna neman sadaka. Na ba su abin da nake da shi amma sun ƙi karba.”
Kuna iya bibiyarmu domin samun Shirye-shiryen bidiyo a YouTube mai suna Whiteblood Multimedia