Labarai
Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano Garo Ya Caccaki Gwamnatin Tarayya

Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Murtala Sule Garo ya caccaki wa’adin da gwamnatin tarayya ta bayar domin cire tsofaffin takardun kudin naira.
Tsohon kwamishinan kananan hukumomin ya koka kan lamarin a lokacin da yake jawabi a taron yakin neman zaben jam’iyyar APC a karamar hukumar Dambatta.
Garo ya ce ba za su zauna su nade hannayensu ba, yayin da mazauna Kano, wadanda galibi ‘yan kasuwa ne ke shan wahala sakamakon mummunar manufar da babban bankin Kasa CBN ya fitar.
“Mutanen Kano sun damu da batun sake fasalin kudin Naira da CBN ya bullo da shi wajen jawo wahalhalu a halin da talakawa ke ciki.” Garo yace.
Murtala Garo ya kuma tunatar da cewa Najeriya na tafiyar da tsarin mulkin dimokuradiyya inda ake mutunta ra’ayoyin mutane sabanin abin da ake samu a mulkin soja.
“A wannan mawuyacin lokaci, mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ka shigar da kara kuma ka yi kira ga babban bankin kasa CBN da gwamnatin tarayya da su sa baki a kan lamarin, domin mulkin dimokradiyya muke yi ba mulkin soja ba.
“Tunda dimokuradiyya ce, mutane ba su cancanci kowane wahala ba.” Ya kara da cewa.
“Ba mu ga sabbin takardun kudin Naira ba, kuma tsofaffin an yi watsi da su. Kano cibiyar kasuwanci ce, suna son mu yi hatsari ne?” Ya tambaya.
“An nemi mu koma gonakinmu kuma mun yi hakan. Tunda mun yi haka, ya kamata gwamnati ta bar jama’a su ci gaba da amfani da kudadensu.” Ya kara da cewa.