Labarai
Wani Mutum Ya Koka Da Yadda Yan Fashi Suka Yiwa Mahaifiyarsa ‘Yar Shekara 65 Fyade

Wani ma’abocin amfani da shafin Twitter, KingAhmed, ya yi kuka a shafukan sada zumunta inda ya koka kan yadda ‘yan fashi suka yi wa mahaifiyarsa mai shekara 65 fyade a jihar Kaduna.
Ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter a ranar Litinin din nan.
Tun da farko KingAhmed ya bukaci ‘yan sanda da su taimaka masa bayan mahaifiyarsa ta kira shi ta shaida masa cewa ‘yan fashi na yunkurin shiga gidan a daren ranar Lahadi.
A safiyar ranar Litinin ne ya saka hoton mahaifiyarsa a asibiti inda ya ce an yi mata fyade kuma a halin yanzu tana jinya.
“Yayin da kuke barci kuna hutawa da daddare, ina nan ina tunanin yadda mutane za su kasance. An yi wa mahaifiyata fyade sau da yawa, kamar yadda kuka shiga gidan mutum, kuka yi musu sata ko kuma kuka yi musu fyade? Ta yaya za ka yi wa mace mai shekaru 65 fyade? Baza ku taɓa ganin salama ba.
“Tana asibiti tana karbar magani. Abin da na samu ke nan bayan na bar gidana na bar kasar mahaifina. Waɗanda suka aikata wannan aika-aika baza su taɓa samun zaman lafiya a duk rayuwarsu ba. Hauka nake yi.”
Lamarin ya faru ne a KekeB kusa da garin Millennium, a Kaduna.
Zaku iya samun labarai da bidiyoyi a kafarmu ta YouTube Whiteblood Multimedia