Connect with us

Labarai

Hukuncin Kotun Koli Tsakanin Ahmad Lawan Da Machina Ya Haifar Da Cece Kuce

 

A ranar Litinin ne kotun koli ta mayarwa da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan takararsa a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC, mai wakiltar Yobe ta Arewa.

A hukuncin da kotun kolin ta yanke na uku zuwa biyu, ta tabbatar da Lawan a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC a gundumar Yobe ta Arewa.

Kotun koli, a cikin hukuncin da ta yanke, ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da kotun daukaka kara suka yanke, wadanda suka tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar APC, bayan da ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayun 2022.

Mai shari’a Centus Chima Nweze, wanda ya zartar da mafi rinjayen hukuncin kotun kolin, ya ce ya kamata Machina ya fara shari’a a babbar kotun tarayya tare da rubuta masa takardar sammaci dangane da tuhume-tuhumen da ya shigar a kan wadanda ake tuhuma.

Sai dai mai shari’a Adamu Jauro da Emmanuel Akomaye Agim sun ki amincewa da hukuncin da aka yanke.

Sun ce babbar kotun tarayya da kotun daukaka kara sun yi daidai a sakamakon binciken da suka yi, wanda ya tabbatar da Machina a matsayin dan takara na kwarai.

Alkalan biyu sun ce an zabi Machina ne bisa ka’ida, saboda zaben fidda gwani na ranar 28 ga watan Mayun 2022, wanda ya samar da shi, an gudanar da shi bisa ka’ida bisa tanadin doka.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Lawan ya ce matakin nasara ce ga jam’iyyar APC a Yobe, da kasa baki daya da kuma dimokuradiyya.

Bayanin nasa na kunshe ne a wani sako da ya wallafa ta shafin sa na Twitter da aka tabbatar.

Tuni dai wannan hukunci ya ci gaba da haifar da cece kuce a tsakanin yan Najeriya, yayin da wasu ke ganin cewa hakan tamkar wata cuwa cuwa ce da aka yi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet