Labarai
‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Matasa Da Ake Zargin ‘Yan Damfara Ne Da Katin Aiki Jarida

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata zamba a tare da samun su da katin shaidar katin aikin jarida na wata tashar rediyo da ke Kano.
Wannan na cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis din nan wanda KakakiHausa Time ta samu.
Sanarwar ta ce a ranar 2 ga watan Fabrairun 2023 mun sami rahoto da misalin karfe 17:00 daga manajan Plaza dake sharada Quarters a karamar hukumar birnin Kano cewa wasu mutane biyu sun je Plazarsu sun sayi buhun shinka kan Naira 33000 kuma suka tura musu kudin ta hanyar taransifa amma sakon na karya ne wato (Fake Alert).
Bayan samun rahon kwamishinan yan sanda na jihar Kano Mamman Dauda psc ya taso tare da umartar tawagar yan sanda karkashin jagorancin SP Abdulrahim Adamu, baturan yan sanda na yankin sharada da su kamo wadanda suka aikata laifin.
Ya ce nan take rundunar ta ziyarci wurin da abun ya faru, inda ta cafke mutane biyu a lokacin da suke kokarin tserewa daya daga cikinsu mai suna Mujahid Kabir mai shekaru 30 dan unguwar Ahmadu Bello Way da Abba Imam mai shekaru 30 da ke gidan Zoo Road duk a Kano.
Sanarwar ta kara da cewa a binciken farko da aka yi an gano wadanda ake zargin dauke da katin shaidar aikin jarida na gidan rediyon Vision FM.
Wadanda ake zargin sun amsa cewa sun je gidan rediyon Vision FM Kano, inda suka sace katin shaidar ma’aikata guda biyu tare da yin irinsu na bogi dauke da sunayensu da hotunansu.
Sun kuma yi ikirarin cewa sun je wannan waje da ke Sharada suka sayi buhun shinkafa sannan suka yi cinikkin karya da biyan kudin karya.
Kwamishinan yan sandan ya bayar da umarnin mika wadanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar (CID) da ke Bamphai domin gudanar da bincike mai zurfi.
Sanarwar ta ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu.