Labarai
Karacin Kudi: Majalisar Magabata Ta Bukaci CBN Ya Gaggauta Daukar Mataki

Majalisar magabata ta kasa ta goyi bayan sabon tsarin kayyade cirar kudi na gwamnatin tarayya amma ta dorawa babban bankin kasar CBN da ya dauki matakin gaggawa na magamce karancin kudade a fadin kasar.
An shawarci gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele da ya samar da sabbin takardun kudi na naira ko kuma a cigaba da amfani da tsofaffin takardun kudi domin saukaka wa ‘yan Najeriya radadin da suke ciki.
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami tare da rakiyar Gwamna Babajide Sanwo-Olu (Lagos) da Darius Ishaku (Taraba) sun yi wa manema labarai karin haske kan sakamakon taron.
Da yake bayyana kudurorin karshe na taron, Malami ya ce manyan batutuwa biyu da aka tattauna sun hada da matakin shirye-shiryen gudanar da babban zabe, wanda shi ne shugaban Hukumar zabe mai maman kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, da Sufeto-Janar na Rundunar ‘yan sanda (IGP), Alkali Baba ya ba da tabbacin shirin da ya dace.
Ya ce bayanin da aka yi kan sabon tsarin hada-hadar kudi da ya hada da sake zayyana wasu nau’o’in Naira, ya haifar da martani da kuma ra’ayi, inda ya ce a karshe ya kamata CBN ya kara himma wajen ganin an samar da isassun kudade a cikin tsarin don samar da kudade masu yawa don rage munanan abubuwan da ke bin manufofin.
“Don haka a karshe, manyan kudurorin guda biyu da suka zo daga tattaunawar majalisar, su ne muke kan gaba dangane da batun zabe kuma mun yi farin ciki da irin shirye-shiryen da INEC da hukumomi suka yi.
“Biyu, dangane da tsarin da aka sake tsarawa na Naira, manufar ta tsaya, amma sai Majalisar ta amince da cewa akwai bukatar a dauki tsautsayi daga bangaren Babban Bankin, dangane da aiwatar da manufofin ta hanyar tabbatar da isassun kudade”, inji shi.