Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Rufe Kwalejojin Kimiyya Da Fasaha

Gwamnatin tarayya ta umurci dukkanin makarantun kimiyya da fasaha na kasar nan da su rufe har sai bayan babban zabe mai zuwa.
Wannan ci gaban ya zo ne mako guda bayan fitar da irin wannan umarnin na rufe dukkan Jami’o’in kasar.
Umurnin na kunshe ne a wata takarda da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta fitar, inda ta umurci babban sakataren hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE), Farfesa Idris Bugaje da ya yi magana da shugabannin kwalejojin.
Wasikar mai dauke da sa hannun Mista I. O Folorunsho, ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu mai kwanan wata 10 ga watan Fabrairu, ta samu ne daga manema labarai a Abuja ranar Litinin.
” Bisa la’akari da damuwar da ake nunawa a kan tsaron ma’aikata da dalibai da dukiyoyin makarantun mu, Ministan Ilimi Adamu Adamu, ya yi shawarwari da hukumomin tsaro da abin ya shafa, ya bayar da umarnin a rufe dukkan makarantun kwalijin kimiyya da fasaha.
” Kuma za a dakatar da ayyukan ilimi tsakanin ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu zuwa Talatar 14 ga watan Maris na 2023, ”wasikar ta karanta.
Ministan ya bukaci shugaban NBTE ya sanar da abubuwan da ke sama ga dukkan cibiyoyin da ke karkashin ayyukan sa. (NAN)