Labarai
An Sanya Muku Ido A Lokacin Zabe, Buhari Ya Fadawa IGP, Da Shugabannin Tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin din da ta gabata, ya shaida wa shugabannin rundunar ‘yan sandan Nijeriya da shugabannin sojoji cewa ‘yan Nijeriya da sauran al’ummar duniya sun zuba musu ido, domin suna da kyakkyawan fata na samar da isasshen tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya don gudanar da babban zaben 2023.
Buhari, wanda ya yi magana a shedikwatar rundunar da ke gidan Louis Edet, a Abuja, a lokacin da yake kaddamar da muhimman kadarori na aiki da rundunar NPF ta siyo, ya yabawa babban sufeton ‘yan sanda, Usman Baba, bisa yadda ya inganta tsarin ‘yan sanda na sake fasalin gwamnatinsa da kuma wasu tsare-tsare da dama da ya kawo wa Rundunar.
Buhari ya ce, “Duk da haka, ya kamata ku tuna da irin babban tsammanin da nake da shi a kan shugabancinku, musamman, dangane da samar da ingantaccen tsaro wanda ba wai kawai zai haifar da ingantaccen tsaro ba a gaban babban zaben, amma zai tabbatar da ingancin aikin.
“A cikin wannan aiki, ina kira ga IGP da haƙiƙa, duk jami’an tsaro da za su taimaka wa ‘yan sanda a harkokin tsaro da za su lura cewa idanun al’umma da na duniya za su kasance a kan ku duka.”
Shugaban ya sake nanata kasancewar rundunar ‘yan sanda mai inganci da kuma mai da hankali wajen karfafa dimokuradiyya da kuma jigon gyaran ‘yan sanda da kuma ajandar sake samar da kayan aiki da gwamnatinsa ta himmatu sosai.
Ya kara da cewa, “Muna gudanar da tsarin dimokuradiyya wanda doka ta tanadar, kuma an san ‘yan sanda a duk duniya a matsayin hukumar da ta fi kowacce alama a tsarin mulkin dimokaradiyya da bin doka da oda.
“Saboda haka, duk wata al’ummar da ke da muradin zurfafa manufofinta na dimokuradiyya da kuma ci gaba da bin doka da oda dole ne ta ba da fifikon ingancin hukumar ‘yan sanda.”