Featured
CBN ya ƙaryata labaran dake yawo cewar bankuna su ci gaba da karɓar tsaffin kudin 500 da 1000

Babban Bankin Najeriya CBN ya musanta rahoton da ke cewa ‘yan Najeriya na iya kai tsofaffin takardun kudi na Naira 500 da 1,000 zuwa bankuna.
Cikin wata sanarwa da CBN din ya ce bai amince wa bankuna su karɓi tsofaffin takardun ba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu bankuna tuni suka fara aikewa da Sakonnin karta kwana ga abokan huldarsu da nufin su miƙa tsaffin kuɗaɗensu.