Featured
Kano: Jam’iyyun siyasa huɗu sun marawa Sha’aban Sharaɗa baya

Adaidai lokacin da babban zaɓe ke ƙara ƙaratowa wanda ya rage ƙasa da kwanaki 21 a gudanar da zaɓen gwamnoni a faɗin ƙasar nan wasu ‘yan takarar gwamna a jihar Kano sun hamɓarar da tafiyarsu tare da marawa ɗan takarar Jam’iyyar ADP Sha’aban Sharaɗa baya.
‘Yan takarar sun janye takarar tasu ne da nufin marawa Sha’aban baya a zaɓen gwamnoni mai zuwa a ƙoƙarin su na ganin sun ceto jihar Kano daga halin da ta tsinci kanta a cewar su.
Hakan dai na cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar ADP ya fitar Abbas Yusha’u, ya ce ‘yan takarar sun fito ne daga jam’iyyu daban-daban da su ka haɗa da Furera Ahmad ta jam’iyyar BT, sai Aishatu Mahmud daga jam’iyyar NRM, sai Ibrahim Muhammad na APGA sai kuma mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APP.
Da yake jawabi yayin karbar ‘yan takarar, ɗan takarar gwamna kuma ɗan majalisar tarayya mai wakiltar birnin Kano, Hon. Ibrahim Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya bayyana jin daɗinsa tare da yin maraba da ƙudirinsu na ɗinkewa waje daya don haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ceto jihar Kano.
Sharaɗa ya kuma yiwa al’ummar jihar Kano albishir da cewa a sati mai zuwa za a ƙaddamar da wani bigeren adana bayanai na yanar gizo da za a yi amfani da shi wajen baiwa ‘yan jihar Kano kimanin Dubu 50 tallafi.
Da su ke jawabi kan maƙasudin barin Jam’iyyun su tare da marawa ɗan takarar jam’iyar ADP baya, ‘yan takarar sunce kyakkyawan ƙudirinsa na tallafawa marayu da matasa da kyawawan manufofinsa ne suka sanya su yanke shawarar su mara masa baya.