Labarai
Kano: Ƴan daba sun farmaki magoya bayan NNPP tare da ƙone musu motoci

Wasu ƴan daba da ake kyautata zaton ƴan bangar siyasa ne, sun farmaki magoya bayan jam’iyyar adawa ta NNPP.
Rahotonni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a unguwar Na’ibawa da ke kan titin zuwa Zaria.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, yayin farmakin, magoya bayan na kan hanyar su ta zuwa garin Kwanar Dan-gora domin tarbar dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Engr Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, yau Alhamis yayin da aka kai musu harin.
Haka kuma ta ruwaito cewa an lalata akalla motoci 10 tare da ƙone wasu yayin farmakin.