Labarai
Rundunar ‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kai Hari Akan Ma’aikatan INEC A Gombe

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe a ranar Asabar din nan ta tabbatar da harin da aka kai kan ma’aikatan wucin gadi na hukumar zabe ta kasa (INEC) da suka yi sansani a makarantar firamare ta Tudunwada, cikin babban birnin Gombe.
Mista Oqua Etim, kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe ya tabbatar da faruwar harin a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a Gombe ranar Asabar.
“Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari. Abin bakin ciki ne matuka, dama ma’aikatan wucin gadi sun matsa da kayan gaban jami’an tsaro. Kuskuren da suka yi kenan.
“Suna kokarin sasantawa ne a gaban sauran abokan aikin da za su tafi tare da tawagar jami’an tsaro daga ofishin INEC.
“Abin takaici ‘yan iska sun yi amfani da hakan. Mun dauki matakai don tabbatar da cewa irin wannan yanayin bai sake faruwa ba.
“Wannan bai taba faruwa ba. Mun shirya cewa yayin da suke barin ofishin INEC a kungiyance, za a yi musu rakiya zuwa wurare daban-daban.”
Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin INEC kan lamarin abun ya ci tura.
Duk wani kiraye-kirayen da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na INEC a jihar, Mohorret Bigun, har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto hakanmu bai cimma ruwa ba.
Jaridar Alkiblah ta ruwaito cewa wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun kuma sace wayoyin salula, da jakar baya da kuma na’urorin cajin waya (Power Banks).