Connect with us

Labarai

Kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku ya yi watsi da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa

Kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yi watsi da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ake ci gaba da fitarwa.

Kwamitin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Dakta Daniel Bwala,

Haka kuma kwamitin ya buƙaci da a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ɗaya daga cikin zaɓin da ya rage wa INEC shi ne ta dakatar da karɓa da kuma sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da take yi.

Daniel Bwala ya ce dakatar da karɓar sakamakon ya zama tilas don shawo kan matsaloli da jam’iyyu suka yi korafi a kai dangane da rashin amfani da na’urar BVAS da kuma kasa tura sakamakon zaɓen zuwa shafin INEC.

Ya ce abin da ya kamata INEC ta yi a yanzu shi ne sanya sabon ranar gudanar da zaɓe a wuraren da aka fuskanci matsalar, da kuma tabbatar da cewa an aika sakamakon zuwa shafin yanar gizo na hukumar zaɓe.

Sanarwar kwamitin ta ƙara da cewa a soke dukkan sakamakon zaɓen da aka sanar har sai lokacin da aka aika sakamakon da aka tattara a rumfunan zaɓe zuwa shafin INEC.

Kwamitin ya kuma ce hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC, ta fito ta yi wa ‘yan ƙasa jawabi kan sahihancin zaɓe da ta gudanar don samun ƙwarin gwiwa ga al’ummar ƙasar da ma na ƙasashen waje.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet