Featured
Buhari Ya Taya Tinubu Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya taya Bola Ahmad Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Wannan sakon ya fito ne ta hannun mai taimakawa shugaban kasa akan harkokin yada labarai Garba shehu.
Buhari yace “Jama’a ne suka zabe shi, shi ne wanda ya fi dacewa da aikin. Yanzu zan yi aiki tare da shi da tawagarsa don tabbatar da mika mulki cikin tsari.”
Ya ƙara da cewa “wannan itace babbar dimokradiya a yankin Africa da aka gudanar tun bayan lokacin juyin mulkin Soja a shekarun baya da suka wuce.
“sakamakon zai taimakawa Dimokradiyya da kasar mu duba da yanda aka Sami kuri’u a sassa daban daban na jihohin kasar nan.