Connect with us

Kasuwanci

Canjin Kudi: Har Yanzu Bamu Da Masaniya Game Da Hukuncin Kotun Koli — CBN

A karo na biyu tun bayan da kotun koli ta yanke hukuncin cewa tsofaffin takardun kudi na Naira 200, da Naira 500 da kuma Naira 1,000 za su ci gaba da zama kudi na hakika domin amfani da su, zuwa karshen wannan shekara, babban bankin kasa CBN ta gaza cewa uffan kan hukuncin.

to sai dai A ranar Asabar din da ta gabata ne wani jami’in babban bankin na CBN ya shaidawa jaridar The Nation cewa, ba a sanar da sashen sadarwa na bankin, wannan umarni ba a hukumance.

Da aka tambaye shi yaushe CBN zai fara sakin kudade ga bankuna, jami’in ya amsa da cewa ba su da wannan bayanin.

KAKAKIHAUSA ta rawaito cewa A ranar Juma’a ne kotun koli ta yanke hukuncin cewa tsoffin takardun kudin na N500, da N1000 da kuma N200 za su ci gaba da zama a matsayin halastattun kudi a kasar nan.

Ba tare da wani sanarwa a hukumance daga CBN ba, bankunan ajiya yanzu haka ba za su iya yin aiki da umarnin kotun ba.

Yanzu dai al’umma na ganin cewa wannan mataki za a kwana biyu kafin ya kai ga yin tasiri, duba da yadda tsofaffin kudin suka shiga banki.

Kuma babu wani tabbaci kan iya fito da su ga abokan hulda, maimakon sabbin da suka samar duk kuwa da yadda suke fama da karancin su.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet