Labarai
Atiku Ya Jagoranci Zanga-zangar Yan Jam’iyyar PDP A Shedikwatar INEC
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ke jagorantar wasu jiga-jigan jam’iyyar a wata zanga-zanga da suka yi a shedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), a yau Litinin.
Atiku ya isa Legacy House shedkwatar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP da karfe 11 na safe inda ya bi sahun sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka taru a harabar suna jiran isowarsa.
Tattakin dai ya tashi ne da misalin karfe 11:10 na safe. Wadanda suka halarci tattakin sun hada da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu da sauran mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC).
Haka kuma masu zanga-zangar sun hada da shugaban kwamitin amintattu na PDP (BoT), Sanata Adolphus Wabara; Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal; Cif Raymond Dokpesi; tsohon gwamnan jihar Adamawa, Boni Haruna da sauran jagorori.
Da yake jawabi ga manema labarai a shedikwatar INEC, gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya ce sun je shedikwatar INEC ne domin gabatar da wasikar su ga alkalan zabe kan matsayarsu kan zaben.
“An yi mana magudi a zaben shugaban kasa kuma mun zo ne domin mu bayyana matsayarmu kan lamarin,” inji Ishaku.
A nasa bangaren, Atiku Abubakar ya ce duk yadda aka gudanar da zaben akwai kura-kurai.
“Mun kai karar INEC daga cibiyar tattara sakamakon zaben cewa bai dace da yadda aka fitar da sakamakon zaben ba amma suka ki,” inji Atiku.
Atiku ya ce za a ci gaba da gudanar da zanga-zangar a kowace rana domin matsawa kan batunsu.
JaridarSOLACEBASE ta ruwaito cewa daga baya an gabatar da wasikar zanga-zangar ga INEC, wanda Festus Okoye da Haruna Muhammad suka wakilta da sauransu.
