Connect with us

Labarai

Atiku ya tanadi lauyoyi 19 don ƙalubalantar zaɓen da ya gabata

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya haɗa tawagar manyan lauyoyi guda goma sha tara da nufin ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabarairu wanda Bola Tinubu ya samu nasara.

Rahotonni sun bayyana cewa, Alhaji Atiku ya yi wa lauyoyin bayani ne yau Laraba a shalkwatar yaƙin neman zaɓensa a birnin tarayya Abuja.

Ɗan takarar, ya buƙaci lauyoyin da su tabbatar wa da kotu dokokin da aka saɓa yayin zaɓen.

Shafin BBC ya bayyana cewa tawagar lauyoyin na ƙarƙashin jagorancin ƙwararren lauya mai zaman kansa JK Gadzama.

Sauran lauyoyin sun haɗa da: Chief Chris Uche da Paul Usoro da Tayo Jegede da Ken Mozia da Chief Mike Ozekhome da Mahmood Magaji da Joe Abraham da Chukwuma Umeh da Garba Tetengi da kuma Chief Emeka Etiaba.

Sauran su ne, Chief Goddy Uche da Farfesa Maxwell Gidado da mai bayar da shawara kan harkokin shari’a na ƙasa na jam’iyyar PDP A.K. Ajibade da O.M. Atoyebi da Nella Rabana da Paul Ogbole da Nuremi Jimoh sai kuma Abdul Ibrahim.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet