Labarai
Kotu Ta Umarci INEC Da Ta Ba Da Damar Amfani Da TVC A Zaben 18 Ga Wata

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis din nan ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta ba da damar yin amfani da katin zabe na wucin gadi, (TVC) a zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da za a gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Mai shari’a Obiora Egwuatu ya bayar da wannan umarni ne a lokacin da yake yanke hukunci a karar da wasu ‘yan Najeriya biyu suka shigar na neman a yi amfani da katin wucin gadi na TVC a babban zabe ba tare da katin zabe na dindindin ba, (PVCs).
Mai shari’a Egwuatu ya ce an bayar da wannan umarni ne a kan cewa masu shigar da kara sun yi rajista kuma bayanansu na cikin ma’adanar bayanai ta INEC.
“An ba da umarnin tilasta wa wanda ake kara (INEC) da ya ba masu kara damar kada kuri’a ta hanyar amfani da katin zabe na wucin gadi da wanda ake kara ya bayar, wadanda ake kara sun kama su da kyau a cikin ma’adanar rajistar masu zabe ta kasa.
” Kotun ta bayyana cewa wadanda suka shigar da karar sun cika duk wasu sharuddan da ake bukata na yin rijistar, saboda haka akwai bayanan su a cikin babban ma’adanar bayanai na wanda ake kara (INEC) da kuma littafin da aka buga da takarda ko kwafi na wanda ake kara. Rijistar masu kada kuri’a, masu shigar da kara suna da damar kada kuri’a ta hanyar amfani da katin zabe na wucin gadi a babban zaben 2023 mai zuwa,” inji alkalin.
Sai dai alkalin ya ce bai iya ba da roko na uku ba wanda shi ne a ba duk wanda ya cancanci kada kuri’a mai TVC damar kada kuri’a saboda ba a shigar da karar a matsayin wakilci ba.
“Ba a kawo wannan kara a matsayin wakilci ba, na ga kaina na kasa bayar da wani taimako bisa ga roko na uku na masu kara.”
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa Kotun ta ce babu wani kaso na doka, da Kundin Tsarin Mulki na 1999 da kuma Dokar Zabe da ta bayyana cewa PVC ce kawai za a iya amfani da ita, amma dokar da ke karkashin sashe na 47 ta tanadi katin zabe.
Da yake zantawa da manema labarai, lauyan masu shigar da kara, Mista Victor Opatola, ya ce hukuncin nasara ce ga duk ‘yan Najeriya da suka sha wahala wajen yin rajistar zabe, sun yi rajistar amma saboda babu laifinsu ba su iya samun katin zabe na PVC kafin zaben ba.
A cewar Opatola, tun da wadanda nake karewa sun cika duk wani bukatu da doka ta tanada amma ba a ba su PVC dinsu ba har sai lokacin tattara PVC din ya kare, bai kamata a bar su su sha wahala ba.