Labarai
Mutane goma sun ƙone a hatsarin mota

Hukumar daƙile afkuwar haɗurra ta Najeriya FRSC ta tabbatar da ƙonewar fasinjoji 10 kurmus sakamakon hatsarin da ya ritsa da su a babbar hanyar Ogbomoso da ke jihar Oyo.
Babban kwamandan hukumar shiyyar jihar ta Oyo Joshua Adekanye ne ya tabbatar da faruwar hatsarin yayin wata tattaunawarsa da manema labarai jiya Alhamis.
Ya ce, mummunan hatsarin ya afku ne sakamakon taho mu gama da wata mota kirar Mazda ta yi da wata mai ƙirar Toyota Hayis da yammacin jiyan.
Haka kuma ya ƙara da cewa gudun wuce sa a da direbobin motocin ke yi da kuma lodin da ya wuce ƙi a ne musabbabin iftila’in.